Yanayin Sarauta Da Masarauta a Wasu Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru

Alhaji Sa’idu Faru, makaɗi ne mai bibiyar tsari da yanayi da kuma al’adun sarauta da masarauta na ƙasar Hausa. Hakan ya sa yake fito da wasu ɗiya a waƙoƙinsa masu nuna yanayin Sarautar sarakuna da kuma masarauta. A yawancin lokaci, Sa’idu Faru yakan fito da manya da ƙananan saƙonni waɗanda suka dace...

Ausführliche Beschreibung

Gespeichert in:
Bibliographische Detailangaben
Veröffentlicht in:Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture Literature, and Culture, 2024-11, Vol.3 (3), p.127-134
Hauptverfasser: Lawal, Nura, Tahir, Muhammad Rabi’u
Format: Artikel
Sprache:eng
Online-Zugang:Volltext
Tags: Tag hinzufügen
Keine Tags, Fügen Sie den ersten Tag hinzu!
Beschreibung
Zusammenfassung:Alhaji Sa’idu Faru, makaɗi ne mai bibiyar tsari da yanayi da kuma al’adun sarauta da masarauta na ƙasar Hausa. Hakan ya sa yake fito da wasu ɗiya a waƙoƙinsa masu nuna yanayin Sarautar sarakuna da kuma masarauta. A yawancin lokaci, Sa’idu Faru yakan fito da manya da ƙananan saƙonni waɗanda suka dace da yanayin sarauta da masarauta, musamman a waƙoƙinsa na fada. Manufar wannan takarda ita ce, fito da yanayin sarauta da masarauta a zubin ɗiyan wasu waƙoƙin Sa’idu Faru. Haka kuma, wannan takarda ta yi amfani da wani ɓangare na tsarin tarken Waƙar Baka Bahaushiya (WBB) wato, Gusau (2023) wajen ƙalailaice yanayin sarauta da masarauta, kamar yadda wannan hanyar nazari ta tanada, sannan kuma an yi amfani da hanyar bi-sharhi, wato (Qualitative Research). Muhammad (2023) ya bayyana nau’in bincike bi-sharhi da bincike ne, na samar da bayanai da suka ƙunshi zurfafa tunani a kan abubuwa mabambanta. Haka kuma, an tattaro ɗiyan waƙoƙin da aka yi misali da su, daga Diwanin Waƙoƙin Baka na Hausa, wato Gusau (2009) da Kundin Digiri na biyu, wato (Labaran, 2024). A wannan takarda an yi amfani da irin wannan tsari aka ƙalailaice bayanan da aka samo, wato wasu ɗiyan waƙoƙin Sa’idu Faru da suka danganci yanayin sarauta da masarauta. A wannan takarda an fahimci Sa’idu Faru yakan lura da yanayin sarauta da masarauta, musamman ta fito da wasu halaye da nagartar da sarki ya kamata a ce yana da su a yayin jagorantar al’ummarsa. Misai, kamar ilimi da kyauta da adalci da iya mulki da faɗar gaskiya da zumunta da iya magana da iya shiga da sauransu. Haka kuma, an lura da yadda Sa’idu Faru ya nuna yadda girma da bunƙasar masarauta sukan ƙara wa Sarki ko sarauta armashi da ɗaukaka da kwarjini a idon mutane da kuma ƙarfin faɗa a ji. Har wa yau, an fahimci cewa, duk wani Sarki da ya haɗa waɗannan yanye-yanye na sarauta da masarauta kamar yadda Sa’idu Faru ya fito da su a zubin ɗiyan wasu waƙoƙinsa, to, zai samu karɓuwa ga talkawansa da sarakuna ‘yan’uwansa da Gwamnati da kuma ƙasa baki-ɗaya. Haka kuma, akasin waɗannan yanaye-yanaye kan rage wa sarki da masarauta daraja da kwarjini a idanun talakawa da sarkuna ‘yan’uwansa da Gwamnati da ma ƙasa baki-ɗaya.
ISSN:2782-8182
2782-8182
DOI:10.36349/tjllc.2024.v03i03.017