Nazarin Wasan Kwaikwayon Soyayya Ta Fi Kuɗi a Mahangar Ra’in Mararanci
Nazarin ayyukan adabin Hausa a bisa wasu ayyanannun ra’o’i abu ne da bai daɗe da bayyana a duniyar nazari ba. Da yawa daga cikin marubuta adabin Hausa sukan yi rubuce-rubucensu ba tare da sanin cewa aikinsu ya yi daidai da wani ra’i ba. Wasu masana suna ganin cewa, wasu nau’ukan ra’in kamar ba su da...
Gespeichert in:
Veröffentlicht in: | Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture Literature, and Culture, 2024-02, Vol.3 (1), p.282-291 |
---|---|
1. Verfasser: | |
Format: | Artikel |
Sprache: | eng |
Online-Zugang: | Volltext |
Tags: |
Tag hinzufügen
Keine Tags, Fügen Sie den ersten Tag hinzu!
|
Zusammenfassung: | Nazarin ayyukan adabin Hausa a bisa wasu ayyanannun ra’o’i abu ne da bai daɗe da bayyana a duniyar nazari ba. Da yawa daga cikin marubuta adabin Hausa sukan yi rubuce-rubucensu ba tare da sanin cewa aikinsu ya yi daidai da wani ra’i ba. Wasu masana suna ganin cewa, wasu nau’ukan ra’in kamar ba su da muhalli a nazarin ayyukan adabin Hausa. Wannan ne ya sa aka yi ƙoƙarin ɗora ra’in Mararanci (Romanticism theory) da manufofinsa a rubutaccen wasan kwaikwayon Hausa domin ganin ko ana iya nazarin ayyukan adabin Hausa ta hanyar amfani da wani ayyanannen ra’i . A wannan aiki an duba manufofin ra’in ne da yadda suke wanzuwa a cikin ayyukan adabi, musamman wasan kwaikwayon Hausa. An bi hanyoyi da yawa wajen tattara bayanan da aka yi amfani da su wajen wannan aiki, waɗanda suka haɗa da karance-karance a littafai domin samun ƙarin haske kan ra’in da aka ɗora aikin, da kuma zaɓo wasan kwaikwayon Soyayya Ta Fi Kuɗi wanda a kansa ne nazarin ya ta’allaƙa. Binciken ya tabbatar da yiwuwar nazarin wasannin kwaikwayon Hausa ta hanyar amfani da ra’in Mararanci. A ƙarshe binciken ya gano cewa, irin waɗannan wasannin kwaikwayon Hausa suna da matuƙar tasiri a kan abubuwan da suka shafi zamantakewar al’umma. |
---|---|
ISSN: | 2782-8182 2782-8182 |
DOI: | 10.36349/tjllc.2024.v03i01.032 |